Kudurin da dan Majalisa mai wakiltar Sabon Garin Zaria na jihar Kaduna, Hon. Garba Datti ya gabatar a zauren Majalisa, idan ya samu damar zama doka zai baiwa Jihohin Najeriya wuka da nama wajen kayyade mafi karancin albashi da kowacce jiha za ta rika biyan ma'aikatanta a maimakon tsarin bai daya karkashin gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Comrade Ayuba Wabba, ya ce kamata ya yi Najeriya tabi sahun kasashen duniya wajen biyan mafi karancin albashi na bai daya.
Ita kuma Kwamarad Hafsat Shuaibu, ta kungiyar yan kasuwa ta Najeriya cewa ta yi idan kudurin ya zama doka, ma'aikata za su shiga halin kaka-nikayi.
A nasa bangaren shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilan kasar, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya ce doka ta baiwa ko wane dan kasa damar gabatar da korafin sa don kalubalantar kowane kudiri ko doka a gaban Majalisar kasar.
Yanzu dai za a sa ido aga wane mataki Majalisar za ta dauka kan sabon kudirin da aka gabatar.
Domin karin bayani saurari rahotan Hauwa Umar.