Mai bai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ya sake jaddada cewa, gwamnatin tarayya na kan bakarta, kuma ba wata kungiya ko mutum da zai mamaye ta kan yin sulhu da ‘yan bindiga dadi ba, inda ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen yaki da kawo karshen batagarin da ke yin barazana ga zaman lafiya a kasar ta Najeriya.
Babagana Monguno ya bayyana hakan ne a yayin zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin tarayya a birnin Abuja, yana mai cewa, gwamnatin tarayya ba ta da sha’awa ko shirin tattaunawa da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da sauran batagarin da ke tada zaune tsaye a kasar don yin sulhu, ya na mai jaddada cewa, yin sulhu da ‘yan ta’adda zai nuna gazawar gwamnati tare da zagon kasa.
Karin bayani akan: Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Babagana Monguno, Nigeria, da Najeriya.
Kazalika, Monguno ya ce, kamar yadda gwamnati ta saba jaddada wa ‘yan kasa, ta na aiki tukuru a yaki da matsalolin tsaro tare da kawo harshen ‘yan ta’adda a kasar.
Babu yadda gwamnati za ta zauna ta tattauna da mutane marasa alkibla da amana, mutanen da ke cigaba da addabar al’umma da ba su ji ba su gani ba da harkokin ta’adanci, In ji Monguno.
Daga karshe dai, Babagana Monguno, ya ce gwamnati za ta yi amfani da duk kayan aiki da ta ke da su da suka hada da na jami’an tsaro, bayanan sirri don kawo karshen miyagun iri a kasar.