Kwana daya bayan da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Ministar jin ƙai, Betta Edu, ta bayyana a ofishin hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Abuja kan zargin ta da bada umurnin tura kudi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun banki na wata mata.
Hukumar ta gayyace ta ne jim kadan bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da ita akan zargin halalta kudin haram.
Kafafen yada labaren cikin gida sun ruwaito cewa ta halarci hedikwatar hukumar EFCC tare da mataimakanta da lauyanta.
A jiya, Litinin 8 ga watan Janairu ne wata sanarwa da Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ya fitar ya sanar da matakin dakatar da ministar da Shugaba Tinubu dauka.
Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kanta.
Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar gudanar da cikakken bincike don tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen amfani da kudaden jama’a da aka ware domin ayyukan jin kai da kuma kawar da fatara.
Dandalin Mu Tattauna