Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Kalubalen Da Zaurawa Suke Fuskanta A Kasar Kamaru, Kashi Na Daya-Mayu-11-2023


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Kwanakin baya, shirin Domin Iyali ya haska fitila kan yawan mace macen aure, dalilan da kuma matakan shawo kan matsalar. A wannan makon, shirin ya fara nazari kan tasirin lamarin musamma ga ma’auratan da kuma ‘ya’yansu, la’akari da korafin da zaurawa a kasar Kamaru su ke yi cewa, suna fuskantar kalubale a fuskoki dabam dabam.

Wakiliyarmu a birnin Yawunde, Maimounatou Sadou, ta tattauna da wadansu zaurawa biyu, wadanda su ka bayyana tushen kalubalen da su ke fuskanta.

Saurari cikakken shirin:

DOMIN IYALI: Kalubalen Da Zaurawa Suke Fuskanta A Kasar Kamaru, Kashi Na Daya
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:45 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG