Washington, dc —
Har yanzu muna tare da Hon Maryam Umar Kofar Mata ‘yar siyasa a jam’iyar APC, da Barrista Amina Umar da ke sharhi kan al’amuran yau da kullum, sai Kwamred Yahaya Shu’aibu Ngogo shima mai sharhi kan al’umuran da suka shafi shugabanci. Kwamred Shu’aibu, a nazarin rawar da mata suka taka a zabukan da aka gudanar a Najeriya da sakamakon ya nuna mata sun sami koma baya.
Saurari tattaunawar da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.