Koma bayan da mata suka samu a zabukan da aka gudanar ya maida hannun agogo baya a fafatukar da matan Najeriya ke yi na neman kaso 35 cikin dari na mukaman siyasa da kuma guraban mulki, batun da muka gayyaci masu ruwa da tsaki domin ganin hanyar warware wannan zare.
Har yanzu muna tare da Hon Maryam Umar Kofarmata ‘yar siyasa a jam’iyar APC, da Barrista Amina Umar da ke sharhi kan al’amuran yau da kullum, sai Kwamred Yahaya Shu’aibu Ngogo shima mai sharhi kan al’umuran da suka shafi shugabanci. Kwamred Shu’aibu, na nazarin rawar da mata suka taka a zabukan da aka gudanar a Najeriya da sakamakon ya nuna mata sun sami koma baya lokaci ya kwace mana inda kuma muka dora ke nan a tattaunawa da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta.
Saurari cikakken shirin: