Kungiyar dilallan man masu zaman kansu ko IPMAN reshen jihar Neja sun kira taron manema labarai jiya Talata inda suka bayyana cewa yanzu kam sun samu sa'ida kan wahalar da suke sha a inda suke zuwa dauko man a kudancin Najeriya.
Alhaji Adamu Erala shugaban kungiyar yace tunda aka cire tallafin, man ya samu koina, kuma dama burinsu ke nan a samu mai a wadace. Yace a sayar masu a farashin da zasu samu riba.
Dangane da masu tada jijiyar wuya akan cire tallafin, Alhaji Erala yace basu san abun dake faruwa ba ne. Yace kuma suna tada jijiyar wuya ne domin wasu sun gaya masu su yi hakan.
Su ma dillalan man a jihar sunce sanadiyar tallafin da ake bayarwa ya sa ana kirkiro karancin man da gangan saboda za'a boye a ba wadansu kana a ki ba wadansu. Yace amma yanzu da aka cire ta zama kasuwace ta bude kuma takara da juna ya tashi. Kowa ya sa nashi farashi. Babu kuma wata saurar wahala wurin dillalan.
Cire tallafin ya kawo karshen karya. Idan NNPC bata ba dillali mai ba yana da damar ya je koina ya saya lamarin da ya sa jama'a sun samu sauki domin man ya wadata a gidajen mai, kuma ana sayarwa a farashin gwamnati na nera 145 kowace lita daya. Saidai wasu suna sayarwa 155 zuwa 160.
Ga karin bayani.