Sabowar takaddamar da ta shiga tsakanin ‘yan rajin dawo da ‘yan matan Chibok da gwamnatin Najeriya, na nuna rashin gamsuwar gwamnatin da yanda kungiyar ke nacewa hukumomin su samo matan, inda ita kuma gwamnatin ke ganin tana daukan matakan da suka dace.
Bayan zargin da jami’an tsaro suka yi cewa ‘yan gwagawrmayan ceto ‘yan matan chibok cewa suna da boyeyen manufa dake barazana ga tsaro gwamnatin Jonathan ta zargin kungiyar ta[# BRING BACK OUR GIRLS]da hana ‘yan matan da iyayensu ganawa da Gwamnati yayin da suka shi go Abuja, kwananan da hakan ke shafawagwamnati bakin fenti.
Dattawan Chibok, ta bakin kakakinsu Dauda Iliya, sun musanta zargin inda yace”gaskiya ba haka bane mu mukace ‘yan matan nan su zo, aka tambayemu muka aika hada da babban wakilinmu can a Chibok, aka samu wadannan ‘yan matan nan a gurguje, idan gwamnati ta naso ta ga ‘yan matan nan tana iya daukan mataki ta gansu, bazata sauna sai an goya taba, baya sun zo su ganin Malala, sai kuma sun ace akan cewa sai sunje an gansu a fadar gwamnati .”
Ya kara da cewa sun rubuta takarda akan cewa suna so a kawo iyaye da ‘yan mata amma ba’a zauna anyi shawara ko za’a yi ko ba za’a yi ba.
Wannan yunkuri na gwamnati in har ya tabbata gaskiya abun marabane inji kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Muhammad Bulama, a ganawan da yayi da manema labaru a Abuja.