A makonnin da suka shude ne jihohin Imo, Abia, Enugu da Legas suka bayyana shirin yiwa duk 'yan asalin arewa dake jihohinsu rajista da samun katin shaidar izinin zama cikin jihohin.
Matakin ya haifar da cecekuce tsakanin 'yan Najeriya da la'akari da cewa ya ci karo da kundun tsarin mulkin kasa.
Yanzu dai kungiyoyin matasan arewa sun fara mayar da martani dangane da shirin na wadannan jihohin. Gamayyar kungiyoyin arewa da ta kunshi kimanin kungiyoyi fiye da hamsin ta kai ziyarar bangirma ga mai martaba sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi II inda ta bashi sakon matsayinta game da batun. Ta bukaci sarkin ya mika sakon ga gwamnan Kano domin shi ma ya mikawa shugaban kasa.
Malam Muhammed Sani Darma daya daga cikin shugabannin kungiyar yace sun dauki matsayin cewa dole mutanen arewa da shugabanninsu su zauna su tabbatar cewa ba'a cigaba da yiwa arewa irin wannan wulakanci ba. Idan har ba za'a daina ba to su 'yan kudu za'a ce su koma jihohinsu 'yan arewa kuma su dawo arewa. A hanzarta a daidaita lamarin domin idan matasa suka balle ba za'a iya shawo kansu ba.
Sarkin ya karbi sakon matasan. Ya kuma basu tabbaci zai idar da sakon ga gwamnan Kano. Sarkin yace Allah yakan shirya a samu kabila daban daban a kasa guda amma wajibi ne a nemi yadda za'a zauna lafiya da juna. Sarkin yayi addu'ar Allah ya ba kasar zaman lafiya da cigaba.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari