Kamar yadda suka bayyana a bana babbar kujera zata kasance nera dubu dari takwas da daya da dari biyar da sittin da daya da kwabo saba'in da bakwai ga wanda zai tashi daga arewa. Daga kudu kuma za'a biya nera dubu dari takwas da tara da dari da talatin da uku da kwabo saba'in da bakwai.
Matsakaiciyar kujera daga arewa zata kama nera dubu dari bakwai da ashirin da uku da dari biyar da sittin da daya da kwabo saba'in da bakwai. Daga kudu kuma nera dubu dari bakwai da talatin da daya da dari da talatin da shida da kwabo saba'in da bakwai.
Karamar kujera kuma daga arewa nera dubu dari shida ne da tamanin da shida da sittin da daya da kwabo saba'in da bakwai. Daga kudu nera dubu dari bakwai ne da casa'in da uku da dari shida da talatin da shida da kwabo saba'in da bakwai.
Idan an kwatanta da farashin bara an samu karin kusan nera dubu hamsin ne akan kowace kujera.
Jami'in yada labaru na hukumar alhazan Uba Mana ya bayyana dalilin da aka samu karin farashe bana. Bana mahukuntan Saudiya sun dauki shawarar cewa kowane alhaji dole a ciyar dashi a Makka da Madina maimakon ciyar dasu kawai a lokacin arafat.
Kazalika hukumar alhazan tana da damuwa da yadda wasu kamfanonin umra ke yiwa wasu masu ibada kumbiya-kumbiya ta hanyar rashin samun biza ko rashin biya masu bukatu. Suna karbar kudaden mutane suna zaluntarsu. Wasu sai an hadasu da hukumar EFCC kafin a kwato kudaden mutane.
Bincike ya nuna cewa 'yan Najeriya ne suka fi kowa zuwa umra a wannan azumin.
Ga karin bayani.