Shugaban yace akwai bukatar ba jami'an tsaro makamai masu inganci da zasu iya fuskantar kalubalen tsaro da kasar ke fama dashi a yanzu.
Shugaban ya kara da cewa bashin da zai ciwo za'a yi anfani dashi a bunkasa horas da jami'an saboda su yi daidai da takwarorinsu dake kasashe da suka cigaba.
Wani dan majalisar wakilai Peter Biye Gumta mai wakiltar mazabar Chibok, Damboa da Gwoza yace yana goyon bayan bukatar shugaban kasa domin karawa jami'an tsaro kayan aiki. Yace duk hanyoyin da za'a bi a yaki ta'adanci zai yi maraba dashi musamman domin abun ya shafeshi. Mazabarshi ce abun ya fi shafa. Yace a yankinsa Damboa, Gwoza da Chibok babu mai kwana cikin gidansa. Yace wasu suna kwana akan bishiyoyi ko cikin duwatsu domin suna tsoron kada azo cikin dare a kwashesu. Lamarin yace yaki ne babba ba kamar yadda ake zato ba. Gwamnati da jama'a sai sun tsaya tsayin daka su yaki 'yan ta'adan. Yin hakan kuma yana bukatar kudi.
Kawo yanzu dai majalisun basu yi muhawara akan bukatar ba amma dan majalisa Ibrahim Bello Rigachukun yace shi fa yana da ja. Yace shi bukatar bata burgeshi ba. Da a ce ana neman bashi ne a karawa 'yansanda kayan aiki da naurori da zasu taimaka su yi aiki kamar na kasashen waje zasu samu karfin gwiwar komawa wurin mutane su fada masu. Amma an ce ana son a karbi bashin kudi gaf da kusa da buga gangar siyasa. Shin wa ya tabbatar cewa idan an ciwo bashin za'a yi anfani dashi akan harkokin tsaro.
Alkalumma sun nuna cewa kawo yanzu kasar ta kashe kudi a harkar tsaro kimanin sama da nera tiriliyon uku tunda aka fara barazanar 'yan Boko Haram cikin shekaru biyar da suka shude.
Ga rahoton Medina Dauda.