Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Shugaban Kasar Nijar Ya Musunta Zargin Tunzura Matasa


Matasan Nijar na zanga zanga
Matasan Nijar na zanga zanga

A jamhuriyar Nijar dan takarar jam’iyyar MDR TARNA a zaben shugaban kasa na 2016 Dr. Adal Rhubeid ya karyatar da wasu rahotannin da aka bayar akansa a kwanakin baya cewa yana tunzura matasa abzinawa su dauki makamai da nufin yiwa gwamnati tawaye.

A taron manema labaran da ya kira shugaban jam’iyyar MDR TARNA Dr. Adal Rhubeid ya tabbatar da cewa ziyarar da ya gudanar a kasar Libya ya gana da ‘yan Nijar mazauna wannan kasar, da kuma jin halin da suke ciki har ma da basu shawara ga yin abubuwan da suka kamata.

Dr. Rhubeid ya nisantar da kansa daga wasu bayanan da wata jaridar kasar waje ta rawaito akan cewa manufofinsa ne, inda ya kira maganar a matsayin shirme.

Wannan dai bashi bane karon farko da zargin aikata laifi mai nasaba da sha’anin tsaro ke hawa kan Dr. Rhubeid, domin ko a washegarin harin da aka kai kan wani Otal din birnin Ouagadougou a watan Fabarairun shekara ta 2016, anyi ta yada jita-jitar cewa yana da alaka da maharan, sai dai daga baya ya karyata labarin.

Saurari Cikakken rahotan Sule Muminu Barma daga Yamai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

XS
SM
MD
LG