Matasa da 'yan kasuwa yanzu suna shiga neman irin abubuwanda zasu yi domin rike kansu da kansu sanadiyar rashin tabbas din rayuwa ganin yadda kungiyar Boko Haram ke kashe mutane daga wurare daban daban.
Wani Alhaji Isiyaku dan kasuwa a birnin Marwa yace tunda maganar Boko Haram ta taso maganar kasuwa ta mutu saboda harkokin kasuwanci sun dagule. Najeriya suke zuwa sayo kaya amma hanyar zuwa sayo kayan babu saboda hare-hare. Mutane na tsoron kada 'yan Boko Haram su harbesu a hanya. Ko a cikin birnin Marwa matakan tsaro sun yi kadan. Alhaji Isyaku ya kira mahukuntar kasar da su taimaka masu.
Malam Yuguda kakakin hukumar tsaro ta jihar Arewa Mai Nisa yace suna daukan wasu matakan karfafa tsaro wadanda yace ba zai bayyana ba.
Ko jiya ma sai da 'yan Boko Haram suka kashe wani sojin ruwa na Kamaru din tare da kashe wasu samari a garin Dambore kana aka kwashe wadanda suka jikata daga wannan sabon harin na jiya. Garin Dambore yana kan iyaka ne da kasar Najeriya inda 'yan Boko Haram suka fi kai hari.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.