A jamhuriyar Nijar an yi bikin tunawa da wannan rana inda gwamnatin kasar ta sanar cewa duk wani yunkurin sayar da fili ko gina gida ba kan ka'ida ba, daga yau ya kawo karshe inji ministan muhallin kasar.
A cewar mahukuntan Nijar bikin wannan ranar tamkar faduwa ce ta zo daidai da zama domin yana faruwa ne a lokacin da gwamnati ke shirin cika alkawuran da ta yiwa 'yan kasarta na gina wa mutane marasa galifu gidaje dubu ishirin da biyar.
Duk da 'yan adawa sunce batun na gwamnati babu gaskiya a cikinsa Alhaji Dan Baba na jam'iyyar PNDS mai mulki yace su sun san abun da suke fadi domin ko suna da abokai masu yawa dake cikin gidajen da gwamnatin Mahammadou Issoufou ta gina na tallafi a wurare daban daban. Har yanzu kuma gwamnati tana nan tana gina wasu cikin jihohi. Yace 'yan adawa ne basa son aikin yayi tasiri.
A bangaren 'yan adawa Alhaji Sirau na jam'iyyar MODEL Lumana ta Hamma Ahmadu suna jira su gani idan har ba fadar baki ba ne kawai.
A bangaren magidanta suna cewa wannan ranar tayi daidai domin samun muhalli yanzu ga jama'a ya zama wani mawuyacin abu. Sunce duk abun da mutum ya samu idan bashi da gida ya zama aikin banza.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.