Hopkins, babban jami'in 'yan sandan Greater Manchester a yau dinnan Talata ya bayyana cewa "Mu na daukar wannan al'amarin a matsayin aikin ta'addanci, kuma a halin yanzu mun yi imanin cewa wani mutum ne ya kai wannan hari na daren jiya,"
Hopkins, ya ce masu bincike sun yi imanin cewa maharin na dauke ne da wani bam hadin gida, wanda ya tayar kuma shi ma ya mutu a wurin.
Firaminista Theresa May, ta ce jami'an 'yansanda da na tsaro sun ce su na kyautata zaton sun san wanda ya kai harin, to amma har yanzu ba su yanke shawarar bayyana sunansa ga jama'a ba.
Daga bisani kuma Rundunar 'Yansanda ta fadi ta kafar Twitter cewa jam'anta sun damke wani mutum dan shekaru 23 da haihuwa a Kudancin Manchester game da wannan harin, amma ba su bayyana alakarsa da harin ba.
Fashewar ta faru ne a farfajiyar dandalin nan na wake-wake da raye-raye na Manchester, wato Manchester Arena, bayan wani shagalin raye-raye da kade-kade na wata ba-Amurkar mawakiya mai suna Ariana Grande.
"Cikin matukar damuwa, kuma daga can cikin zuciyata, na ke cewa ina mai mika jaje na," a cewar Grande a kafarta ta Twitter bayan fashewar, inda ta kara da cewa, "Ban ma san abin cewa ba."
Facebook Forum