Koriya ta Kudu (KTK) tace makwabciyarta Koriya ta Arewa (KTA) ta sake gwada wani abu “mai kama” da makami mai linzame.
Ofishin babban hafsan hafsoshin Koriya ta Kudu yace a yau Lahadi ne aka cilla wannan makamin
daga lardin Pyongyang dake kudancin kasar, kuma, bisa ga dukkan alamu, rokan ayyi tafiyar da ta kai ta km 500 kafin ya fada a cikin teku.
Ita ma fadar shugaban Amurka ta White House ta tabattarda cewa Koriya ta Arewa, ta harba wannan makamin, koda yake Amurka tace zango da ya ci baiyi nisan rokoki ukku na karshe da Koriya ta Artewa, ta harba ba.
Kamfanin dillacin Labaran AP yace shugaban Koriya ta Kudu, Moon Jae-in ya kira taron gaggawa na majalisarsa ta tsaro don tattaunawa wannan matakin da Koriya ta Arewa, ta dauka.
Facebook Forum