Alhaji Yusuf Katambe shugaban jam'iyyar PNDS Tarayya reshen jihar Tawa ya bayyana wa jama'a a birnin Tawa cewa shugaban kasar ne ya dauki kudurin sakawa 'yan majalisun 37 sake shiga takara kai tsaye ba tare da shiga takarar tankade da rairaya ba ta jam'iyyar PNDS.
To saidai wasu 'ya'yan jam'iyyar na ganin ba'a yi masu adalci ba. Kudurin da shugaban kasar ya dauka tamkar ya kashe dimokradiya ne. A cewarsu ya kamata a bar kowa ya zabi wanda yake so ya tsaya takara a zaben shekarar 2016.
Wani jigo a yam'iyyar PNDS Alhaji Tsalha Dan Bau yace akwai sauran mukamai da yawa da mutane zasu iya nema ba lallai sai na majalisar tarayya ba. Akwai mazabu da yawa inda jama'a zasu zakulo wanda suke so.
A bangaren jam'iyyun dake hamayya da PNDS Tarayya su murna suka yi da matakin da shugaban kasa ya dauka na danne dimocradiya. Alhaji Isa Mare kakakin jam'iyyar Model Lumana Afirka ta Hamma Ahmadu reshen jihar Tawa yace su taro zasu yi su bar kowa ya zabi wanda yake so ya tsaya takara. Su zasu yi dimokradiya ba kamar PNDS ba. Matsayin jam'iyyar shugaban kasar a jihar Tawa tamkar ya taimakawa 'yan adawa ne kana ya jawo cecekuce cikin tashi jam'yyar. Su kam 'yan adawa gaba ta kaisu gobarar Titi.
Ga karin bayani.