Tsohon Minista na musamman a fadar shugaban kasa a zamanin Tandja Muhammadu, Albade Abuba, shi ne shugaban rikon kwarya na wannan sabuwar jam’iyya.
“Sakamakon da ya fito daga kotu, bai bamu gaskiya ba, shi ya sa mu kuma muka ce za mu kirkiro jam’iyyar da za ta kumshi duk wadanda mu ka yi aiki da su tun daga shekarar 2013.” In ji Abuba.
Albade Abuba da maogya bayansa sun sha fama kan takaddamar shugabanci da ta barke a jam’iyar MNSD, lamarin da ya kai ga zuwa kotu, inda aka bas u Abuba rashin gaskiya.
Jam’iayyar ta MPR, ta ce za ta maida hankali wajen ganin ‘yan Nijaer sun samu biyan bukatunsu idan har suka kafa gwamnati.
“Za mu kama ma jama’ar Nijar duka, ta yadda za mu kawo musu sauyi cikin rayuwarsu da yaddar Allah, ta yadda za mu samu mu bunkasa kasar ta mu ta yadda za mu fidda da ita daga matsalar talauci da ta ke fuskanta.” In ji Abuba.
Domin jin cikakken rahoton, ga Souley Moumouni Barmah da karin bayani: