Matakin da gwamnan Yamai Hamidu Garba ya dauka na korar 'yan kasuwa daga kewayen babbar kasuwar birnin ya gamu da fushin 'yan kasuwan.
A cikin takardar da ya aima kamsu ya basu nan da biyar ga watan gobe da su tara nasu -i-nasu, su fice daga inda suke kasuwanci abun da ya harzukar dasu suka fantsama yin zanga zanga.
Gwamnan ya zargi 'yan kasuwan da haddasa cunkoso lamarin da sautari ke kaiga hatsarin ababen hawa.
Saidai 'yan kasuwan sun ce rashin wurin zuwa ne ka sasu mamaye wuraren.
Wasu sun ce babu inda zasu domin su 'yan kasa ne. Suna da takardu na yin kasuwanci inda suke. Sun babu wata doka da zta iya korarsu.
Alhaji Sani Shekarau ya kira gwamnati ta su sassauta su samu yadda zasu warware matsalar cikin ruwan sanyi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani