A wani sabon rahoto da kungiyar sa idon ta fitar, ta ce sojojin sun yi 'barin wuta akan masu zanga-zanga a yankin na Oromia ba tare da basu kashedi ba, ko kuma daukar matakin da ba na karfi ba don shawo kansu. Rahoton kuma ya ce yawancin wadanda aka kashe din dalibai ne, ciki har da yara wadanda basu kai shekaru 18 da haihuwa ba.
Kungiyar sa idon ta kuma ce ‘yan sanda sun kame dubban mutane tun lokacin da aka fara wannan zanga-zangar, kuma yawancinsu har yanzu suna nan a tsare ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba, ko basu damar ganin lauyoyinsu ko iyalansu.
Zanga-zangar dai ta samo asali ne bayan da gwamnatin kasar ta yi yinkurin fadada iyakar Adis Ababa, babban birnin kasar. Masu zanga-zangar sun yi fargaban cewa shirin zai daidaita manoman yankin Oromia.
Tuni dai gwamnatin kasar ta soke shirin a watan Janairun shekarar nan amma an cigaba da yin zanga-zangar har tsawon watanni saboda abinda masu zanga-zangar suka kira “matakin zalunci”
Har zuwa yanzu dai babu wani murtani da gwamnatin ta Habasha ta maida akan wannan rahoton.