Bisa ga alamu babbar jam'iyyar adawa ta jamhuriyar Nijar ta mika kai bori ya hau saboda ta amince ta shiga gwamnatin hadaka da shugaba Issoufou ya yi mata tayi makon jiya.
Bayan sun kwashe tsawon Asabar da ta gabata suna muhawara da kace-nace da cecekuce, masu ra'ayin a dama dasu a gwamnati sun samu rinjaye.
Dan majalisar dokokin kasa Murtala Alhaji Mamuda shi ya dauki sanarwar karshen taron. Yace matsalar tattalin arziki da matsalar tsaro suka sa 'yan jam'iyyar suka amince da tayin gwamnati. Cikin mambobi dari da arba'in da takwas hudu ne kawai basu yadda ba. Saboda haka zasu shiga su taka tasu rawar a gwamnatin.
Sakataren watsa labaran jam'iyyar na kasa baki daya Tambura Issoufou dake adawa da shawarar shiga gwamnati yace hujjojin da uwar jam'iyyar ta bayar domin shiga gwamnatin hadaka da Issoufou Mahammadou ke shirin kafawa ba masu gamsarwa ba ne. Yace me ya sauya zani da har zasu shiga gwamnain. A ganinsa babu wata hujja illa talaucin zuciya da na kudi.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.