Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power tayi kira ga jami’an Sudan ta Kudu da su binciki wannan ta’asa kuma a hukunta wadanda aka samesu da laifin wannan aika-aikar na cin zarafin ma’aikatan agajin. Tace akasarin lokaci gwamnatin Sudan ta Kudu tana zuba ido ta kyale sojojinta suna kashe mutuane kuma suna abkwa wa mata.
Tace wannan hari da aka kai akan wa’yannan mutane masu karfin zuciya masu niyar taimakawa jama’ar Sudan ta Kudu, ko shakka babu wannan hari ne na take ‘yancin bil adama. Tace akwai bukatar kare duk wani farin hula da bai san hawa ba bai san sauka ba.
Ms Power ta kara da cewa wadanda suka aikata wannan abu, sun yi ne da zummar musgunawa mutanen da suka sadaukar da rayukansu don su taimakawa mabukata a Sudan ta Kudu ba tare da tunanin irin haduran dake tattare da shiga kasar don su bada agajin gaggwa ga mutanen Sudan wadanda yaki ya jefasu cikin mawuyacin hali.
Wannan harin da aka kai ran 11 ga watan Yulin wannan shekara, an dauki kamar tsawon sa’oi ukku ana kai shi akan otel din Terrain Hotel, wanda galibin mazaunasa duk mutanen kasashen ketare ne.