Yace dakarun Kamaru sun shiga kauyen sun yi binciken kwakwaf kana sojoji suka fatattakesu kodayake sojansu guda ya ji rauni.
Yace harin da 'yan ta'adan Boko Haram suka kai inda jami'an tsaro suke wata alama ce dake nuna cewa duk da yake suna cikin damuwa amma suna nuna cewa har yanzu suna da sauran karfin tada zaune tsaye. Yace su sani cewa sojojin na nan cikin shirin ko ta kwana domin kare martabar kasarsu.
Jamhuriyar Kamaru tana cikin kasashen da sojojinta suna cikin sojojin kawancen yaki da kungiyar ta Boko Haram. Ko satin da ya gabata, kasar ta aika da sojojinta can bakin iyaka da jihar Arewa Mai Nisa bayan da wasu 'yan kunar bakin wake su biyu suka tarwatsa kansu a garin Limani wanda ya yi dalilin mutuwar mutane goma sha uku.
Isa Ciroma ya cigaba da cewa sojojin kasar sun kai samame a wasu kauyuka takwas akan iyakar kasar inda suka kashe 'yyan kungiyar Boko Haram tare da kame wasu cikinsu da yawa. Sun kuma kubutar da wasu mutanen da 'yan ta'adan suka kame suna garkuwa dasu. Hakazalika sun lalata dakunan da suke sarafa bamabamai har guda goma.
Wasu daga cikin 'yan Boko Haram din sun yi kokarin tserewa. Yayi imanin cewa yakarsu da Najeriya da Nijar ke yi ya sa 'yan Boko Haram din matsawa kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.
Saidai kuma tashe tashen bamabamai da kunar bakin wake sun zama manyan matsalolin da kasar ta Kamaru ke fama dasu. Wannan ya sa kasar Kamru girke dakarunta a wuraren da 'yan kungiyar suka fi kai hari, musamman wuraren da suke da iyaka da Najeriya kana ta hana taron jama'a a masallatai musamman a lokacin watan Ramadan da ya gabata.
Ga karin bayani.