Inji kakakin rundunar kawancen sojojin, Kanal Muhammad Dole, dalili ke nan da sojojin suka kaddamar da wani sabon farmaki mai taken "Operation Gama Aiki" domin kakkabe 'yan ta'adan daga yankunan da suka labe.
Rundunar tace samun wani sabon mafaka ya yiwa kungiyar Boko Haram wuya. Sabon shirin da ya kunshi sojojin Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru ya bada damar samun nasarori a faggen daga a gabzawar da aka yi a garuruwan Doron Nera da Faidinjumba da Yebi Kasugiya da dai sauransu. Nasarar ta bada damar fataktakar 'yan Boko Haram daga bangaren Najeriya. Haka kuma an 'yanto wasu kauyukan tsibirin tafkin Chadi daga hannun 'yan ta'adan Boko Haram din.
Rundunar kasashen kawancen tace a yayinda ta kai farmaki, dakarunta sun hallaka 'yan ta'ada kimanin talatin da daya aka kuma lalata masu kayan aiki tare da gano wani rumbun makamai.
Cikin kayan da aka kwace daga hannun 'yan Boko Haram akwai mota kirar Hilux dauke da bindiga mai sarafa kanta da bindigogi kirar AK 47 da gurneti 21 da bindigogin harba roka da wasu dimbin bindigogin na daban.
Sojojin hadin gwuiwar kimanin biyu sun rasa ransu sanadiyar farmakin yayinda wasu guda goma suka samu raunuka. Kwamandan rundunar Janar Lamidi Adeosun ya umurci askarawansa dake shiya ta uku ta Baga da su kasance cikin shirin ko ta kwana domin karya lagwon 'yan ta'ada. Sannan ya bukaci fararen hulan dake zaune a yankin su ba sojoji hadin kai a wannan yakin tare da kira ga jama'a kada su yi kasa a gwuiwa wajen sanar da 'yansanda duka bakuwar ijiyar da ba'a yadda da ita ba.
Ga karin bayani.