A jamhuriyar Nijar, ana ci gaba da maida martini bayan harin da kungiyar Bobo Haram, suka kai garin Bosso, akarshen makon jiya.
Kungiyoyi na Majalisar dinkin duniya, na ci gaba da daukar matakai domin tallafawa mutanen garin na Bosso, wadanda suka yi kudun hijira sanadiyar wannan mummunar lamarin, kamar yadda jami’in, majalisar dinkin duniya mai kula da ‘yan gudun hijira a jamhuriyar Nijar Muhammadu Gide ke cewa.
Jiya shugaban Nijar Issoufou Mahammadou, ya kai wata ziyarar gaggawa zuwa N’djamena, babbar birnin kasar Chadi, inda ya gana da shugaba Idris Derby, ganawar da shuwagabanin tsaron kasashen biyu suka halarta da kuma shugabanin rundunonin tsaro masu jagorancin askarawan kasa da kasa dake fafatawa a kewayen tafkin Chadi da kungiyar Boko Haram.
Shugabanin sun ce ba zasu sa idanu suna ganin ‘yan Boko haram, na aikata irin wannan danyen aikin da suka gudanar a garin Bosso ba, wanda kuma ya sabawa addinin Musulunci, kuma sun sha alwashin cewa anan gaba zasu kai farmakin a yita ta kare da kungiyar ta Boko Haram.
Malam Muhammadu, jami’in majalisar dinkin duniya mai kula da ‘yan kudun hijira a Nijar, yace su kungiyar ne mai taimakawa gwamnati, kuma yadda gwamnati keso a bisa doka haka za’a yi.