Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan kasuwar mai kan kara farashi ba tare da wata sanarwa ba.
Hakika farashin litar fetur a yanzu a Najeriya ba iri daya ba ne ko da kuwa a gari daya ne inda wani wajen a kan samu ratar da ta kan kai Naira 15 har ma fiye da haka.
Kazalika man fetur da a kan yi amfani da shi a cikin kasa ya fi tsada a yankunan arewacin Najeriya da ke nesa da bakin teku.
Kwarerren ma'aikacin fetur da ya yi aiki a cibiyar hakar fetur ta GULF OF GUINEA, Dr. Mubarak Ibrahim Mahmud ya ce zabin shi ne mataki na gaggawa da zai taimaka wajen saukaka farashin man.
Shi ma tsohon karamin ministan kudi Dr. Yarima Lawan Ngama ya sha nanata muhimmancin kafa matatun fetur daga 'yan kasuwa har daga bisani aka kaddamar da matatar fetur mai zaman kanta ta Dangote a Lagos.
Kmafanin man fetur dai ya sanar da nasarar samun danyen mai a rijiyoyin Kolmani da ke jihar Bauchi da Gombe sai kuma zuwa kaddamar da aikin hako man a jihar Nasarawa.
Aikin hakar man a yankin Borno ya samu cikas lokacin da fitinar Boko Haram ta tsananta.
Tsohon shugaban matatar kamfanin fetur ta Kaduna da ke kamfen din karfafa matatar Warri, Fatakwal da Kaduna, Injiniya Kailani Muhammad na cewa marigayi Firimiya Ahmadu Bello ya yiwa yankin arewa adanar arzikin mai da ya dace a kara matsa kaimi wajen cin gajiyar sa.
Matatun fetur din Najeriya ba sa tace mai da zai wadaci kasar don haka kusan kacokan kasar kan shigo da mai daga ketare dake zama da dan karen tsada don hauhawar farashin dala.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna