Hakan ya biyo bayan rijiyar Kolmani ta farko da aka fara aiki a kanta a 1999 inda aka samu iskar gas, yanzu kuma aka toni fiye da kafa dubu 10 da muradun kaiwa kafa dubu 14,270 don kammala aikin rijiyar ta biyu.
Sabon shugaban kamfanin fetur Mele Kyari ya ci alwashin bunkasa kamfanin da irin wannan aiki kazalika da tada matatu 4 kafin karewar wa'adin mulkin shugaba Buhari a 2023.
Lamarin aikin gano man ya Kara fitowa fili ne a watan jiya yayin mika ragama a hukumance da tsohon shugaban kamfanin fetur NNPC Maikanti Kachalla Baru ya yi ga sabon shugaban Mele Kolo Kyari.
Bayanai daga aikin nemo man na nuna samuwar man a yankin Neja har zuwa tafkin Chadi wanda aikin ya samu tsaiko a yankin kan iyaka saboda illar Boko Haram da kan sace ko barazana ga rayuwar jami'an binciken man.
Alamu dai na nuna samun man zai zaburad da samun kudin shiga a arewa, a maimakon dogaro kacokan kan noma da kiwo
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya
Facebook Forum