ABUJA, NIGERIA - Masana a fannin albarkatun mai na ganin hakan ya zo a kan gaba kuma zai kawo kari wajen samun kudadden shiga ga kasar idan har aka kamalla aikin yadda ake tsammani.
Kaddamar da aikin tona man a matakin farko kuma a hukumance a jihar Nasarawa da gwamnatin Najeriya ta yi yau a karkashin shugaba Muhammadu Buhari na zuwa ne kasa da watanni 5 da kaddamar da makamancin aikin na rijiyar Kolmani da ke kan iyakar jihohin Bauchi da Gombe, lamarin da akasarin masu ruwa da tsaki a jihar suka yi marhaba da shi suna kuma fatan aikin zai kawo ci gaba ga jihar da kasa baki daya.
A jawabin da ya yi ta bidiyo a lokacin bikin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yana mai farin cikin kaddamar da wannan gagarumin aikin rijiyar Ebenyi-A da ke tsakiyar karamar hukumar Obi a jihar Nasarawa. Ya kuma wannan mataki ya yi daidai da yadda ake ci gaba da gudanar da aikin neman hakar danyen mai da iskar gas a yankunan da ke kan iyakokin kasar da suka hada da tafkin Chadi, tafkin Dahomey, yankin Anambra, Calabar, Sokoto, Bida, Binuwai da dai sauransu.
Gwamna Abdullahi Sule, shi ne mai masaukin baki, ya ce wannan ci gaba da aka samu wani lheri ne daga Ubangiji da kuma kokarin da dukkan masu ruwa da tsaki daga bangaren gwamnati da sauran al’umma suka yi.
Basaraken Osuko na karamar hukumar Obi Alhaji Aliyu Dangiwa Orume, ya bayyana matukar farin ciki da ci gaban da aka samu, yana mai cewa tun ba a kamalla aikin rijiyar ba an samar wa dimbin mutane ayyukan yi yana kuma fatan cewa za a samu karin ayyukan yi idan aka kamalla aikin baki daya.
Masu bibiyar al’amurra dai na kyautata zaton cewa idan aka kamalla ayyukan rijiyoyin man Kolmani da Obi tattalin arzikin Najeriya zai habbaka kuma za a samu karin ayyukan yi ga matasa masu zaman kashe wando a kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf: