Wadannan cututtuka ba wai kawai suna saurin kashe mutane bane, jinyarsu na da tsadar gaske. Binciken da aka kafe a mujallar The Lancet, ya kimanta cewa cikin shekaru 15 masu zuwa, kasashe masu tasowa zasu kashe sama da dalar Amurka Triliyan bakwai kan wadannan cututtuka.
Shekaru uku da suka gabata, shugabannin duniya sunyi alkawari rage samun mace-mace daga ire-iren wannan cututtuka da ake samu da kashi daya cikin uku zuwa shekarar 2030.
A taron babban zauren MDD na ranar Alhamis, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya, Dakta Tedros Adhanom, ya ce kasasehn duniya ‘kasa da rabi zasu samu iya cimma wannan manufa, yana mai kiran shugabannin duniya da su bayar da himma kan wannnan batu.
Facebook Forum