Shugaban kasar Najeriya ya bayyana damuwar sa akan yadda ake ci gaba da samun matsalolin tsaro a duniya, a lokacin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.
Yace abin takaici abubuwan da ke kawo barazana da koma baya ga tsaro da zaman lafiyar duniya da "muka tattauna a bara" har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Ya kuma tabo batun rashin tsaro da ake fama da shi a nahiyar Afrika da yankin Asiya musamman rikicin Syria da Yemen da Falasdinu da ma ayyukan ta'addanci na cikin gida kamar boko haram da sauran su.
Akan batun mummunar kisan da akayi wa kabilar Rohinygya a Myanmar,shugaban na Najeriya ya yabawa Majalisar Dinkin Duniya akan kokarin kawo karshen wahalhalun da 'yan kabilar musulmin Rohingya suka fada ciki.
Shugba Buhari ya kuma yi magana akan yaki da cin hanci da rashawa inda ya ce dole ne a yaki cin hanci da rasahwa, saboda su suke hana kasashe ci gaba tare da jefa su cikin rashin tsaro da kuma kwararar kudaden haram.
Saurari rahoton Baba Yakubu Makeri....
Facebook Forum