Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Coronavirus Na Janyo Kalubale Ga Hakkin Bil’adama - Guterres


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce barkewar cutar coronavirus na dada zama matsala a bangaren kare hakkin bil’adama

A wata sanarwa da aka fidda a yau Alhamis, Guterres ya yi kira ga gwamnatoci da su tabbata sun samar da cibiyoyi da kayayyakin kiwon lafiya wadanda duk jama'a zasu iya samu, kuma tallafin karfafa tattalin arziki na taimaka wa wadanda annobar ta fi shafa, sannan kowa da kowa na da damar samun abinci da ruwa da kuma matsugunni, cewar sanarwar.

Guterres ya ce, "muna ganin yadda cutar ba ta nuna banbanci, amma tasirinta ya ya kawo hakan, lamarin ya nuna rauni sosai wajen raba ayyukan al'umma da kuma rashin daidaiton tsari dake kawo cikas a hanyar samun ayyukan. Dole ne mu tabbatar an magance wadannan matsalolin ta hanyar da ta dace, a cewarsa.

Sannan ya kara da cewa, a duk abinda zamu yi, kada mu manta cewa kwayar cutar ce barazana ba mutane ba.

Sakon shugaban Majalisar na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an kiwon lafiya a fadin duniya ke gargadin cewa yayin da wasu kasashe suka samu ci gaba sosai a yaki da cutar har suka fara sassauta matakan hana zirga zirga, har yanzu ba a gama yaki da kwayar cutar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG