Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce yawancin annobar coronavirus a Turai, a ta bakinsa, “da alamu ta fara lafawa,” to amma yayi gargadin cewa “wannan cuta za ta kasance da mu zuwa wani lokaci mai tsawo.”
Lokacin da yake gudanar da taron manema labarai da ya kan yi kullum a Geneva game da cutar COVID-19, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nemi a yi taka-tsantsan da cewa “yawancin kasashe har yanzu suna mataki na farko na annobar” su kuma da annobar ta fara afka masu, “yanzu sun fara ganin cutar na fara dawowa.”
Tedros ya ce dokar hana fita da sauran matakan bayar da tazara sun taimaka wajen shawo kan yaduwar cutar a kasashe masu yawa, sai dai kuma jin dadin shawo kan annobar shine babban hatsarin da za a fusakanta.
Facebook Forum