Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya a yau Talata ya ce muddin kasashen duniya suka yi garaje wajen dage matakan takaita zirga-zirga, to kuwa akwai hadarin yiwuwar sake dawowar cutar coronavirus.
Dr. Takeshi Kasai, daraktan hukumar lafiya ta duniya mai kula da yankin yammacin Pacific, ya fada a wani taron manema labarai cewa “yanzu ba lokaci ne da za a yi sako-sako ba," ya kamata mu shirya kanmu domin tunkarar wata sabuwar hanyar rayuwa.
Sakon na gargadi yana zuwa ne a yayin da gwamnatoci a fadin duniya suke duba lokacin da ya dace su sassauta dokokin hana yaduwar cutar, wadda ta lakume rayukan jama’a a fadin duniya tsawon watanni.
Firayim Ministan Italiya Giuseppe Conte ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, gwamnatin kasar zata bada sanarwar shirinta nan da karshen mako bayan aiki da kwararru domin tsara yadda za a sake bude al’amura sannu a hankali.
Ita ko majalisar dokokin kasar Birtaniyya tana daukar matakai daya bayan daya na komawa aiki bayan dogon hutu.
Facebook Forum