A yayin da kasashen Afrika ke Allah wadai da wariyar da ake nuna wa ‘yan Afrika a kasar China sanadiyar annobar coronavirus, kungiyar ‘yan Nijer mazauna China ta yi kira ga hukumomin kasar da su dauki matakan da zasu ba ‘yan Nijer damar samun kulawar da ta dace ta bangaren diflomasiyya don kare su daga dukkan wani wulakanci.
A wani taron manema labarai da suka kira a birnin Yamai, wasu shugabannin kungiyar ‘yan Nijer mazauna China, wadanda annobar cutar coronavirus ta hana komawa kasar ta Sin, sun bayyana irin halin kaskanci da wulakancin da ‘yan Afrika ke fuskanta a birnin Guangzhou. Lamarin da suka ce ya rutsa da wasu ‘yan Nijer kamar yadda Mamman Bachir Dan China, kakakin kungiyar ya shaida.
Hulda a tsakanin China da Nijer wani abu ne da hukumomin kasashen biyu suka sha shailar cewa kyakkyawa ce, wacce ta ta’allaka akan harkokin kasuwanci, aiyukan hakar ma’adinai, gine-gine, ilimi, noma, da sauransu. Wannan ya sa ‘yan Nijer mazauna China suka bukaci mahukuntan Nijer su dauki mataki don kare ‘yan kasar kamar yadda Najeriya ta yi domin mutanenta dake zama a China.
Saurari Karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum