Jami’an sojin kasar Chadi, sun tabbatar da cewa dakarunsu sun kashe mayakan Boko Haram kusan 1,000 yayin wani farmaki da suka kai a wasu tsibirai a yankin Tafkin Chadi.
Wata sanarwa da Kakakin rundunar sojin kasar Kanar Azem Bermandoa ya fitar ta talbijin ta nuna cewa, kwana takwas dakarun suka kwashe suna kai hare-hare kan ‘yan ta’addan a tsakanin Chadi, Najeriya, Nijar da kuma Kamaru.
Bermandoa ya kara da cewa, an kashe dakarun Chadi 52 sannan an jikkata wasu kusan 200 a lokacin farmakin.
Matakin sojin na zuwa ne bayan wani hari da mayakan Boko Haram din suka kai kan wani barakin soji da ke Bohoma inda suka kashe sojoji sama da 92.
Jami’an sojin kasar sun ce harin shi ne mafi muni da aka taba kai wa kan dakarunsu.
Mayakan na Boko Haram sun kashe dubun dubatar mutane sannan sun tilastawa wasu miliyoyi tserewa daga gidajensu cikin sama da shekara goma da suka kwashe suna kai hare-hare a kasashen da ke yankin Tafkin Chadi.
Facebook Forum