Adadin masu dauke da cutar coronavirus a Ghana ya kai 408, a cewar ma’aikatar ayyukan lafiyar kasar ta GHS.
A shafinta na Twitter, ma’aikatar ta ce an samu karin mutum 30 a baya-bayan nan.
A ranar Alhamis shugaba Nana-Addo-Dankwa-Akufor-Addo, ya bayyana cewa kasar na da adadin mutum 378.
Yanzu an samu bullar cutar a takwas daga cikin yankunan kasar 16, bayan da masu dauke da ita suka kai 408.
“Daga cikin mutum 408 da aka tabbatar suna dauke da cutar, 205 an gano su ne bayan bincike da aka yi, 88 daga binciken da aka tsananta, 115 daga matafiya da aka kebe a yankunan Accra da Tamale, a cewar ma’aikatar ayyukan lafiya ta GHS.
Mutum takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu a kasar ya zuwa yanzu.
Facebook Forum