Wani shahararren mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyo Gil Bailey, dan asalin kasar Jamaica ya rasu sakamakon cutar coronavirus a Birnin New York. Masoyan shirye-shiryensa daga wurare dabamdaban na cikin alhinin mutuwarsa.
Kafofin watsa labarai sun ce Bailey ya rasu ne a birnin New York yana da shekaru 84 a duniya a jiya Litinin sanadiyyar matsalolin cutar ta coronavirus. Bailey yayi suna sosai ta rediyo a matsayin muryar jama’ar Jamaica da sauran 'yan yankin Carebiya tsawon shekaru 50.
Shirin da Bailey ke gabatarwa a rediyo a duk ranar Asabar, yana da dimbin masu saurare a kwaryar birnin New York, hadi da New Jersey da Connecticut, da suke da yawan al’ummar 'yan Carebiya, musamman ma 'yan Jamaica.
Ministar al’adu, harkokin shakatawa da wasanni ta Jamaica Olivia Grange, ta yi alhinin mutuwar, tana mai cewa ita abokiyar Bailey ce kuma sun yi aiki tare shekaru masu yawa.
Facebook Forum