A yayin da kasashen Afrika ke Allah wadai da wariyar launin fata wanda ake zargin wasu kasashe da nunawa Afrikawa a China sanadiyar annobar Coronavirus, kungiyar ‘yan Nijar mazauna China ta yi kira ga hukumomin kasar da su dauki matakan da zasu bai wa ‘yan Nijar din damar samun kulawar da ta dace a diflomasiyyance don kare su daga dukkan wani wulakanci.
A taron manema labaran da suka kira a birnin Yamai dangane da wannan lamarin, wasu shuwagabanin kungiyar ‘yan Nijar mazauna China wadanda annobar cutar Coronavirus ta hana wa komawa kasar ta China ne suka sanar da jama’a halin kaskanci da kuma wulakancin da Afrikawa ke ciki a Gwangzu.
Wani mai suna Mamman Bashir Dan China, wanda shi ne kakakin wannan kungiyar, ya shaida wa Muryar Amurka halin da wasu abokansu da ke Chinar ke ciki.
Ya ce “abokanmu da ke can suna aika mana hotunan yadda ake sa su zama a daki na mako 2 duk da cewar basu da cutar kuma a hana su abinci.”
A cewarsa an fara yi musu hakan ne bayan da wasu ‘yan Najeriya biyu masu cutar suka gudu daga wurin da ake tsare masu Coronavirus.
“Bakaken fata ne kawai ake tsarewa kuma ba za a ma yi musu gwaji ko suna da cutar ba ko a’a.”
Hulda a tsakanin China da Nijar wani abu ne da hukumomin kasashen 2 suka sha cewa kyakkyawa ce kuma an danganta hakan ne da kasuwanci irin na ayyukan hakar ma’adanai da ayyukan gine-gine.
Abin da ya sa ‘yan Nijar mazauna China suka bukaci ma’aikatan Nijar su dauki mataki don kare ‘yan kasar kamar yadda Najeriya ta yi domin ‘yan kasarta da ke zaune a China.
Saurari cikakken rahoton a sauti.
Facebook Forum