Biyo bayan umurnin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar na rufe wasu manyan birane a matsayin wani mataki na dakile yaduwar cutar coronavirus (COVID-19) dake shafar numfashin bil'adama, mahukunta a babban birnin kasar, daya daga cikin biranen da umarnin ya shafa na shirye-shiryen aiwatar da umarnin.
Kwamishinan 'yan sandan birnin Abuja, Bala Chiroma, ya shaida wa Muryar Amurka cewa, tuni suka tanadi isassun jami'an 'yan sanda da kayan aiki, ciki har da karnuka don ganin an bi wannan umarni.
Bala Chiroma ya ce ya kyautu jama'a su bi wannan umarni ko don
kare lafiyarsu da ta sauran jama'a, musamman duba da yadda kusan kullum
ake ci gaba da samun sabbin wadanda cutar ke kamawa, yana mai jaddada
cewa duk wanda ya ki bin wannan umurni a birnin, to su a shirye suke su
tilasta bin umarnin.
Kwamishinan 'yan sandan ya kuma ce sun riga sun tsara wuraren da zasu toshe da kuma inda za a kai jami'an 'yan sanda don hana kai da komon da bai zama tilas ba.
Shima Ministan babban birnin tarayyar Muhammadu Musa Bello, tuni ya
fara daukar matakai. A cewar kakakin ministan Abubakar Sani, Ministan zai kira wani taron gaggawa da manyan jami'an tsaron birnin don tabbatar da an bi umurnin gwamnati.
Tun a makon jiya ne dai Ministan na birnin Abuja ya bada umarnin rufe illahirin manya da kananan makarantu, da kasuwanni, da ma wuraren ibada, tare da takaita tarukan jama'a akan ko ma wanne irin dalili.
Sai dai kuma wasu daga cikin mazauna birnin dake rayuwar hanu baka hanu
kwarya sun nemi gwamnati ta dauki matakin tallafa masu, musamman idan aka yi la'akari da cewa wasu kullum sai sun fita zasu samun abin sawa a bakin salati.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum