Gwamnatin jihar Kano ta bi sahun wasu kasashen duniya wajen yaki da annobar cutar coronavirus inda ta sanya dokoki da matakan kariya daga yaduwar cutar.
Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umurnin hana taron jama'a, da rufe makarantu, da ma’aikatun gwamnati, gami da tashoshin motoci da ke zirga-zirga daga jihar Kano zuwa wasu jihohin.
Sannan daga cikin matakan kariyar da gwamnatin ta dauka har da umurni gudanar da feshi a fadin jihar don tsaftace muhalli da kuma kariya daga yaduwar cutar.
Kwamishinan yada labaran jihar, Muhammad Garba ya bayyana dalilin da ya sa gwamnati ta dauki irin wadannan matakan, musamman na yin feshi. Ya kuma ce gwamnatin jihar na ba kwararru, da masana tare da ma'aikatan kiwon lafiya goyon baya, domin ganin an wayar da kan al'umma.
Jami'in kungiyar masu safara tsakanin jihohi, kuma jami'in ladabtarwa akan wadanda suka karya doka, Musbahu Alin Gwale, ya ce duk wani dan kungiyar da aka kama ya karya doka to tabbas zai fuskanci fushin kungiyar ko a dakatar dashi baki daya.
Shugaban Hukumar KAROTA ta jihar Kano, kungiyar dake daya daga cikin kwamitin da aka kafa akan annobar cutar coronavirus, honarabul Baffa Babba Dan Agundi, ya ce tuni gwamnatin jihar Kano ta hana zirga-zirgar ababen hawa daga wata jiha zuwa jihar, sai dai ta bada damar shigo da magunguna, abinci, kayan masarufi, da kuma masu larurar rashin lafiya.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Baraka Bashir.
Facebook Forum