Hukumomi a jihar Bauchi sun umurci jami’an tsaro da su tabbatar da jama’a suna bin dokar hana fita a wani mataki na dakile yaduwar cutar Coronavirus.
A halin da ake ciki an samu karuwar mutum guda wanda aka tabbatar ya na dauke da cutar ta Covid-19 a jihar.
Hakan na nufin a jihar Bauchi akwai mutum uku yanzu masu dauke da cutar.
A jawabin da shugaban kwamitin yaki da cutar ta Coronavirus da kuma zazzabin Lassa a jihar, Sanata Baba Tela ya gabatar a asibitin Bayara, ya fayyace halin da ake ciki da kuma matakan da aka dauka na tabbatar da hana yaduwar cutar Coronavirus a jihar baki daya.
Ya ce "a yanzu mun yi gwaji 99, a cikin na mutum 23 da aka dawo da su ne aka samu karin mutum 1 da ke da cutar."
"A yanzu an killace shi kuma an fara yi masa magani kuma mutum biyun wadanda dama ake tsare da su masu cutar, muna fatan cikin mako mai zuwa za a sallame su," in ji Sanata Baba Tela.
Gwamnatin ta kuma bayyana wani mataki wanda ta ce zai kawo wa jama'a sauki a jihar.
A cewar gwamnatin ta Bauchi, ta ware kwana biyu wato Laraba da Asabar daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma domin barin mutane su fita su yi cefane.
Ta kuma bayyana cewa duk da za a bar mutane su fita, za a tilasta musu barin tazara tsakaninsu da kowa.
Gwamnatin ta Bauchi ta jaddada cewa wannan matakin na zama a gida zai jefa mutane da dama cikin yunwa, saboda haka ne ta yanke shawarar ware kwana biyu domin bai wa mutane damar samun abincin da zasu ci.
Saurari cikakken rahoton a sauti.
Facebook Forum