Cibiyar kula da dakile cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da sabbin alkaluman masu dauke da cutar coronavirus, inda jihar Legas ta kara samun mutane sha takwas, sha biyu a jihar Kano, biyu a jihar Katsina, sai jihohin Neja da Delta da kowannensu aka samu karin mutum daya.
A halin yanzu, gaba dayan adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai dari hudu da bakwai, bayan da aka samu kari mafi yawa a rana guda na mutane talatin da hudu.
A baya bayan nan an samu rahoton mutuwar mutum daya daga jihar Kano a arewacin Najeriya sakamkon kamuwa da cutar coronavirus.
Cibiyar NCDC ta kuma sanar da cewa mutane dari da ashirin da takwas sun warke daga cutar coronavirus a Najeriya amma kuma wasu su sha biyu sun rasu.
Babban Jami’in cibiyar NCDC Dr. Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa an samu ingantacciyar hanyar gudanar da bincike akan ‘yan Najeriya don tantance ko suna dauke da cutar ko kuma a’a. Akalla yanzu ana gwada kusan mutane dubu uku a kowacce rana.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum