Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Majalisar Dokokin Amurka Ta Ja Hankali Kan 'Yan matan Chibok


Chibok school girls
Chibok school girls

'Yar majalisar wakilan Amurka Frederica Wilson daga jihar Florida, ta sake jan hankalin al'umma akan illar cutar coronavirus, musamman al'ummar dake fuskantar barazanar kungiyar Boko Haram.

A cikin dogon jawabin da ta yi na tunawa da cika shekaru shida da sace 'yan matan Chibok, 'yar majalisar ta ce idan ba a tashi tsaye ba, kungiyar Boko Haram na iya amfani da annobar da duniya ke fama da ita wajen ci gaba da sace 'yan mata.

'Yar Majalisa Frederica S. Wilson: Ba Za Mu Manta Da 'Yan Matan Chibok Ba
'Yar Majalisa Frederica S. Wilson: Ba Za Mu Manta Da 'Yan Matan Chibok Ba

Shekaru shida kenan da 'yan kungiyar Boko Haram suka girgiza duniya bayan da suka yi garkuwa da wasu dalibai ‘yan mata su dari biyu da saba’in da shida a Najeriya.

Cutar coronavirus na kara wa kungiyar ta’addancin karfi, yayinda suke ci gaba da zama ake barazana ga rayukan ‘yan mata. Saboda haka, dole ne kasar Amurka ta gaggauta daukar mataki.

Yin garkuwa da ‘yan matan Chibok masu yawa da kungiyar Boko Haram ta yi, ya sa fitattun mutane, shugabannin duniya da wadanda ke damuwa da al’umma a fadin duniya gangami da lakabin " a dawo mana da ‘yan matanmu’’ ko "Bring Back Our Girls’’, ya zame wani karamin kaso daga dimbin mata da maza da suka bace tun da kungiyar ta fara aikin ta’addanci a Najeriya, a shekara ta dubu biyu da tara.

'Yan Matan Chibok
'Yan Matan Chibok

Gwamnatin Najeriya ta kiyasta akalla mata dubu tara zuwa dubu goma sha uku ne suka bace, yayin da kungiyar Red Cross ta kasa da kasa da ta Najeriya suka yi kiyasin dubu goma sha bakwai, ciki har da yara dubu bakwai.

Ban da ‘yan mata kanana da take aurarwa, kungiyar ta Boko Haram ta yi garkuwa da kananan yara maza da take horar da su aikin soja, sun kuma hallaka dubban mutane, yayin da suka raba mutane miliyan biyu da dubu dari biyar da muhallansu a Najeriya, Chadi, Kamaru da Nijer.

A cikin wadanda aka yi garkuwa dasu akwai Hauwa 'yar shekaru goma sha biyar. Duk da shike ba ta san tsawon lokacin da ta yi a tsare ba, har ta haihu a inda aka garkame ta ba, ta kuma sha azaba lokacin da ta kubuta daga hannun Boko Haram zuwa Maiduguri, har ya kai ga mutuwar danta dan watanni shida. Ta ma kasa binne shi ko ta yi makoki saboda gudun wadanda suka yi garkuwa da ita.

Wadanda suka kubuta daga hannun Boko Haram da suka hada da mata da yara sun kasance da raunin zuciya, suna kuma fuskantar kalubalai da suka hada da gami da gurbatacciyar gwamnati, matakan kiwon lafiya marasa inganci, da tsangwama da suke fuskanta a yankunansu, har ila yau zuwan wannan annoba na iya sa yanayin ya kara muni, kamar yadda ake fuskanta lokacin tashin hankali.

'Yan Matan Chibok Da Suka tsira daga 'yan Boko Haram
'Yan Matan Chibok Da Suka tsira daga 'yan Boko Haram

Duk da yake cutar coronavirus ba ta bazu sosai ba a Najeriya da nahiyar Afirka kamar yadda sauran kasashen duniya ke fuskantarta, barkewar cutar a Najeriya zai yi mummunan lahanin da zai shafi sauran kasashen duniya.

Najeriya, kasar da wata cibya da ake kira “World Poverty Clock” ta ba ta suna ‘’cibiyar talauci ta duniya’’ a shekara ta dubu biyu da goma sha takwas, ita ce ke da mafi yawan ‘yan gudun hijira da suka shigo daga kasashen waje, da ‘yan gudun hijirar cikin gida da kuma ‘yan gudun hijirar da aka tilasta musu barin gidajensu.

Akasarin ‘yan udun hijirar suna wasu sansanoni a Maiduguri, fadar jihar Borno dake Najeriya, inda sansani daya ke makare da dubban ‘yan gudun hijira, a wuri mai kazanta inda kuma cututtuka ke iya saurin yaduwa. Irin wannan yanayin yana da hadari sosai musamman a lokacin annoba a duniya.

A Maiduguri, a missali, babu dakin kula da marasa lafiya mai tsanani da na’urar shakar iska, kuma yayin da kasashen duniya ke tara magunguna da kayayyakin tsafta, abinda aka fi bada fifiko a sansanonin shine samar da bukatun tilas da suka hada da abinci da mafaka.

Najeriya na kan yaki da cutar zazzabin Lassa kuma yawancin ‘yan kasar a ciki da wajen sansanonin, ba zasu iya killace kansu ba saboda basu da ruwan famfo da zasu wanke hannuwansu.

Duk da karuwar tattlin arziki a kasashen yankin Afirka, dake kusa da hamada, kungiyar Boko Haram tana rike da karfinta a Najeriya dake da rauni da tarihin gurbatacciyar siyasa, da rashin daidaiton rabon arzikin kasa.

Kungiyar Boko Haram ta wargaza illahirin yankin tafkin Chadi, ta kuma rusa ikon gwamnati a yankin da gurgunta jarin kasashen duniya da kuma tallafin kasashen waje.

Har a yau, Najeriya ta fi bada fifiko kan ayyukan dakaru a yankin, amma bayan fiye da shekaru goma, gwamnatin ta kasa yin nasara akan Boko Haram da daidaita alamura a yankin.

Karfin soja ba zai yi nasara kan Boko Haram ba, dole sai Najeriya ta yi amfani da hanyoyi dabamdaban don shawo kan musabbabin rashin tsaro da rashin daidaito ta hanyar tallafa wa alumma da kudade, samar da ci gaba, ilimi, da sauya tunanin wadanda ke kai hare hare.

Samar da manufofi da zasu hada kan alummar yankunan da suka hada da mata da 'yan mata da sarakuna, shine zai daidaita alamura a yankin. Dole a samo hanyoyin hana tsangwama don a hada wadanda suka tuba daga ayyukan ta’addanci da iyalansu, a kuma maida wadanda suka kwaci kansu daga hannun masu garkuwa da ‘ya’yansu zuwa garuruwansu.

Rashin mafita, da ci gaba da nuna wariya da rashin karuwar tattalin arziki zai iya sake maida wadanda suka tuba daga kungiyar Boko Haram da wadanda suka kubuta sake komawa hannun yan Boko Haram. Sanya mata da ‘yan mata na da muhimmanci wajen cimma nasara a yankin.

A yau da ake tunawa da shekaru shida da sace 'yan matan Chibok, muna (?) kiran abokan aikinmu a dukan majalisun biyu, mu sake sanya Amurka ta kasance kan gaba wajen daga murya don karfafa mata da yammata a duniya.

Mu roki gwamnatin Najeriya, da hadin gwiwr yankuna da kasashen duniya, ciki har da gwamnatin Amurka da hukumar tsaro, su kara kaimi wajen yin nasara akan 'yan ta'adda, su kuma aiwatar da tsarin sheka biyar don shawo kan barazanar tsaro da Boko Haram da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a yankin.

Idan har kasashen duniya basu sake zage damtse wajen samar da daidaituwar lamura a yankin ba, to lallai idan har cutar coronavirus ta bazu a Najeriya, zata yi illar da Boko Haram bata yi ba, wato hallaka abokan gaba da kafa daular musulunci ta yan taadda.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG