Dumbin ‘yan ciranin kasar Mali da suka makale har tsawon watanni uku a Nijar saboda rufe kan iyakoki da aka yi sanadiyyar cutar COVID-19, sun koma gida.
A farkon makon nan ne hukumar da ke kula da ‘yan cirani ta duniya ta samu damar mayar da ‘yan cirani 179 zuwa Mali, wadanda aka ajiye su a wasu cibiyoyin hukumar da ke Yamai da birnin Agadez a Nijar.
Cikin makonnin biyu da suka gabata, hukumar da ke sa ido kan masu kaura ta Majalisar Dikin Duniya, ta yi nasarar mayar da wasu ‘yan cirani 43 zuwa Burkina Faso sannan ta mayar da wasu 58 zuwa Jamhuriyar Benin.
Facebook Forum