Wani babban jami’in sojin kasar Sudan ta kudu, wanda ake zargi da hannu a harbe wasu fararen hula uku har lahira ya rasu.
Sojan ya rasu ne sanadiyyar raunukan da ya samu a lokacin arangamar da ta kai ga harbe fararen hular.
Wata majiya daga ofishin Shugaba Salva Kiir ta ce Lual Okook Wol Kiir, ya rasu ne a daren ranar Laraba a wani asibiti da ke Juba.
Majiyar ta ce an bugawa Wol Kiir wanda dan uwane na jiki ga Shugaba Salva Kiir karfe a kai yayin da wata zazzafar takaddama ta kaure tsakaninsa da wasu mazauna unguwar da ake kira Sherikat.
A cewar majiyar, wacce ta nemi da a sakaya sunanta, Sojan ya yanke jiki ya fadi ne bayan da aka buga masa karfen, lamarin da ya sa dogarawan da ke tsare lafiyarsa suka bude wuta a unguwar.
Wani shaida mai suna Juuk Thiong Juuk, ya ce sojan ya yi kokari ne ya kwace wani fili mallakar mutanen unguwar a lokacin da lamarin ya faru.
Facebook Forum