Shugaban yankin Somaliland Muse Bihi ya ce hukumomi a Mogadishu ne babban kalubalen da yankin ke fuskanta a yinkurinsa na samun amincewar duniya a matsayin cikakkiyar kasa mai diyauci, shekaru 29 bayan da yankin ya balle daga kasar Somalia bayan da aka hambare shugaban soji mai kama karya Siad Barre.
A wata hira da Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka ya yi da shi, Shugaba Bihi ya yi kira ga al’ummar duniya da ta amince da halalcin diyaucin Somaliland, yana mai cewa hanyar warware matsalar Somaliland ita ce kawai shugabannin kasar Somalia da ke birnin Mogadishu da kuma al’ummar duniya su amince da abin da ya kira “abin bai kawuwa na kasancewar kasashe biyu.”
(Jami'an gwamnatin Somaliland)
Ya kara da cewa tun bayan da yankin na Somaliland ya ayyana ‘yancin kansa daga Somalia, mun yi duk abin da mu ke iyawa don samun amincewar duniya.
Mu na shugabanci ne bisa tsarin demokaradiyya, mu na da madafun cigaba masu inganci da ake tafi da su cikin lumana, kuma ta bangaren tattalin arziki ba za mu zama wata nawaya ga duniya ba, duk da haka an ki amincewa da mu, kuma babu wanda ya fito ya ce ba mu cancanci diyaucin ba,” a cewar Shugaba Bihi.
Facebook Forum