Biyo bayan taron Majalisar tattalin arzikin Najeriya ta ‘kasa. ‘Daya daga cikin ‘yan kwamitin, gwamna Nasiru El-Rufa’i, yace cikin wata uku masu zuwa in Allah ya yarda Najeriya za ta fita da cikin halin ‘ka ‘ka na kayi na tattalin arzikin ‘kasa.
Gwamna El-Rufa’i ya ce, yanzu haka fannin Noma da masana’antu sun bunkasa, amma fannin Mai shine ya sauka ‘kasa sai dai tun da ‘yan tsagerun yankin Niger-Delta sun daina barnata bututun Mai cikin watanni uku za a fita daga karayar tattalin arziki a Najeriya.
Ga lamuran noma gwamna Aminu Masari, ya ce bana ba za a samu cikas ta bangaren taki ba, inda yace bana taki zai wadata.
Masana lamuran tattalin arziki da kudi irinsu kwamishinan kudi na Gombe, Hassan Mohammad, na yabawa komawa zabin Noma da gwamnatin Najeriya ta yi baya ga Man Fetur.
Shima mai sharhi ta yanar gizo kwamrad Baban Sharif Gumel, ya ce hana shigo da abinci cikin Najeriya daga ketare yayi fa’ida,
Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum