Rikicin dai ya samo asali ne bayan da kungiyar ‘daliban kwalejin ta gudanar da zabenta, inda aka samu rashin jituwa tsakanin ‘daliban game da sakamakon zaben da aka samu.
Da yake yiwa Muryar Amurka ‘karin haske game da lamarin, kwamishinan yada labarai Alhaji Abdullahi Idris, ya ce ganin cewa ‘daliban zasu yi rikici yasa aka hanasu yin zaben ranar Talata, jiya Laraba kuma ‘daliban suka fara tayar da hankali, har ta kai ga fita wajen makaranta da zuba duwatsu akan hanya har kusan wani shingen sojoji, da zummar hana motoci wucewa.
Sojojin dake wajen sunyi kokarin shawo kan ‘daliban kafin karasowar ‘yan sanda amma basu sami nasara ba, hakan yasa suka fara harbe-harbe. A cewar Kwamishinan yada labarai, mutane biyar ne aka raunata, mutum guda kuma yana cikin mawuyacin hali, baki dayansu ana kula da lafiyarsu.
Jami’an tsaro dai sun kama wasu ‘dalibai da suka hada da mata da maza. Haka kuma an rufe makarantar bayan sallamar duk mutanen dake cikin Kwalejin.
Domin karin bayani ga hirar Mustapha Nasiru Batsari da Kwamishinan yada labaran jihar Bauchi.
Facebook Forum