Kungiyar manyan ma'aikatan kanfanoni masu sarrafa man fetur ta Najeriya PENGASAN ta bi sawun kungiyar kasashe masu sarrafa man fetur OPEC wajen kira ga gwamnatin Najeriya ta fadada aikin neman albarkatun man fetur a arewacin kasar tare da bukatar ta sauya tunanin ta na saida matatunta ga 'yan kasuwa.
Masani kan makamashi Dokta Mohammed Ibrahim ya gabatar da bukatar kungiyar a taron kungiyar a Yola fadar jihar Adamawa a cikin wata kasida da ya gabatar yana bayanin kokarin da kasashe da suka ci gaba ke yi na samar da makamashi da zai maye gurbin man fetur da gas don kaucewa gurbatar muhalli da fargabar da ake da ita na karewar man fetur a doron kasa nan da shekaru masu zuwa, Dokta Ibrahim ya ce bincike ya nuna duniya zata ta ci gaba da anfani da man fetur da gas duk da fargabar da ake da ita kuma ba sai a tekuna kadai ake samun makamashin mai ba.
Da yake tsokaci kan aniyyar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna na ci gaba da aikin neman man fetur da ta dakatar a tabkin Chadi sakamakon ayukan ta'addanci a yankin, shugaban kungiyar Mayan ma'aikatan kanfanoni da ke sarrafa man fetur da gas ta kasa Komred Francis Ojebode Johnson ya ce kungiyar na goyon bayan wannan mataki na gwamnatin tarayya biyo bayan nasarar fatattakar 'yan kungiyar ta'adda ta Boko Haram amma ya ce kamata ya yi gwamnati ta sauya tunanin ta na sayar da matatun wa 'yan kasuwa.
Taken taron kungiyar manyan ma'aikatan kanfanoni dake sarrafa man fetur na bana shine "Makomar Matatun Man Fetur da Gas na Najeriya da Neman Karin Rijiyoyin Man Fetur".
Ga Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum