Wasu iyayen daliban da suka yi karatu a kasashen waje sun kai kokensu gaban majalisar dokokin Najeriya don neman Mafita sakamokon wannan mataki da hukumar kula da harkokin likitoci a kasar ta dauka na tilasta wa duk wanda ya karanci aikin likita a kasashen ketare yin wasu kwasa-kwasai na tsawon watanni shida bayan biyan kudade sama da miliyan daya kafin samun damar rubuta jarabawar samun lasisin fara aiki a kasar.
Wannan lamari dai ya biyo bayan wata sanarwa da hukumar ta fitar da ke nuni da cewa matakin zai soma aiki ne daga ranar 21 ga watan Disamban wannan shekara ta 2021.
Sanarwar ta kuma ce duk dalibin dake shirin zana jarabawar karbar lasisin fara aikin likita sai ya yi kwasa-kwasai na tsawon watanni shida kafin samun damar zana jarabawar.
Haka kuma sanarwa ta yi kari da cewa sai dalibi ya biya adadin kudi da ya kai Naira miliyan daya da dubu dari hudu, wanda wasu iyaye suka bayyana a matsayin babban tashin hankali ga iyayen daliban wadanda akasarinsu alfarma ce ko kuma gwamnati ce ta dauki nauyin karatun 'ya'yan nasu zuwa kasashen waje din.
Hajiya safiya Umar Gwandu uwa ce ga daya daga cikin daliban da suka yi karatun aikin likita daga kasar Sudan, ta ce tun da suka sami wannan sanarwa suka shiga tashin hankali a matsayinsu na iyaye wadanda ba su da karfin daukar wannan nauyi.
A cewarta, wasu daga cikinsu sun yi ritaya daga aiki, wasu ma ba su yi karatu ba, wadanda ma suka yi karatun albashinsu ba yawa, ga kuma sauran hidindimu na rayuwar yau da kullum, amma kuma a ce cikin sati uku su nemo makudan kudade su biya.
Ita ma Hajiya Sadiya ta yi kari da cewa "wannan tsari da aka fito da shi bai yi ba domin gwamnati ce ta dauki nauyin karatun mafi yawan a kasashen waje, sun dawo kuma yanzu a ce sai an biya wasu kudade kafin su mori ilimin da suka samu daga kasar da suka yi karatu?"
To sai dai ana su bangaren shugaban hukumar kula da harkokin likitoci a Najeriya Farfesa Abba Waziri Hassan ya bayyana dalilansu na daukar wannan mataki.
Ta ce sun fahimce cewa mafi yawan daliban da suka yi karatu daga kasashen wajen idan sun dawo Najeriya, cewa akwai wasu cututtuka da ba su san da su ba, wasu ko allurar rigakafi na wasu cututtuka ba su iya bayarwa ba, don haka suka ga dacewar ba su horo na musaman har na tsawon watanni shida don tattabar da kwarewarsu da kuma kare mutanen da za su duba kafin ba su lasisin fara aiki.
Tuni dai majalisar dokokin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki su ka yi zama na gaggawa kan batun, tare da bukatar hukumar ta canja tsari da samar da sauki ga dalibai.
Fannin kiwon lafiya a Najeriya dai na fama da karancin ma’aikata sakamokon fita kasashen wajen da suke don samun aikin yi inda suke ganin anfi daraja su.
Saurari Rahoton Shamsiya Hamza Ibrahim: